Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M21
==Gandun Hikima 6==

1. In za ka shuka ka ji shuka irin kwarai,

Ko ba ka nan bayanka dole ta girbo.

2. Kome kake kak kyautata shi a duniya,

In an kira sunanka dole a dibo.

3. Kome ka samu dibi jeka ka adana,

In ka rasa wata rana jeka ka debo.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124