Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 5 | 1M213
==Mala'iku A Afirika==

Mu nan Hausawa abin da muka sani mala'iku a sama suke, duk da yake a akwai wadanda ke a kasa, amma su kansu saukowa suke yi daga sama, kodayake akwai wadanda ke tare da mutane wadanda ke rubutun ayukansa, amma su ma komawa suke sama.

To amma ashe akwai wasu masu imani da mala'iku sabanin irin namu imani, su a tananinsu akwai nahiyoyin da ke da irin nasu mala'iku, daga cikin irin wadannan nahiyoyi akwai nahiyarmu ta Afirika.

Irin wadannan namu mala'iku kamar yadda wasu suka yi imani, suna iya tashi daga nan su tafi can inda suke su taimaka masu ga harkokinsu.

To a kan irin wannan imani da irin wadannan mala'iku, wata mai bai wa shugaban Amuruka shawara a kan harkokin addini, watau Paula, ta ce ta yi addu'a, kuma tana fatan irin namu mala'iku su tashi daga nan Afurika su sauka a Amuruka don taimaka wa Trump wajen lashe zabe.

Mu ba zabe ya dame mu ba, abin da ya dame mu shi ne irin wannan imani na irin wadannan mutane wanda ya saba da irin namu imani.

Wannan fa gudummawa ce babba ga masu nazarin al'ada, sai a adana inda ya kamata.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124