Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 5 | 1M215
==Kukan Mawakan Gargajiya==

"Idan aka yi wasa nan gaba sai an nemi makada da mawakan Hausa na gargajiya an rasa saboda yadda aka yi musu rikon sakainar kashi".

Wannan zancen Alhaji Ibrahim Dankwairo ne, watau dan shahararren mawakin nan Musa Dankwairo.

Kuka ne yake yi kan yadda harkar wakar gargajiya ta lalace, ba a samun kome a cikinta, har yake ganin cewa nan gaba ba za a koma jin duriyar mawakin gargajiya ba.

To Alhaji Ibrahim, sai a ce ka yi wa kanka dabara da ka daina waka, amma idan kukan mutuwar irin wadannan wakoki kake yi, sai dai ka mutu wurin kuka, don darajarsu ba za ta dawo ba har abada.

Ba wai bacewar wakar gargajiya ma ya kamata ka yi wa kuka ba, a'a, kukan bacewar Bahaushen gargajiya ya kamata ka yi, don ka sani, nan gaba sai an nemi Bahaushen gargajiya an rasa, ba wai wakar gargajiya ba.

Ka yi hakuri don Allah.

Ga cikakkiyar fira nan da aka yi da wannan bawan Allah. BBC Hausa ta yi ta, sai a duba don a kara ba shi hakuri.

labarai-55025305

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124