Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 8 | 1M218
==Almarar Raha==

Wannan ci-gaba ne ga kokarin Jangwarzo kan almara da misalanta. Misali kawai ne daya daga nau'ukan, mai son sanin dukansu ya duba rubutu mai lamba. 1060M19

Ga misalin:

Wani kwarto ne ya rasa dabarar da zai yi ya je gidan abokiyar harkarsa da ta yi aure a wani kauye. A karshe dai ya je kauyen, kuma ya yi shigar mata da dare ya yi sallama ya shiga gida. Kowa bai gane shi ba in ban da mutumniyarsa.

Mijinta ya shigo, sai ta tarbe shi tana cewa gwaggo ce ta kawo mana ziyara.

Mai gida ya yi murna sosai, ya tarbi gwaggo yadda ya kamata. Ya koma zaure ya kwana, ya bar kwarto da matarsa a dakinta.

To da yake matan kauye na fita daukar ruwa tun da safe, ta bar kwartonta na bacci. mai gida ya zo ya yi wa gwaggo barka da kwana. Ya ga kwarto ya mimmike kwance a kan gadonsa yana bacci. Haushi ya kama shi matuka. Ya ma rasa hukuncin da zai yi. A karshe dai ya gano matarsa ta fi wannan kwarto laifi, don haka sai ya yanke shawarar ya soma halaka ta, sannan ya dawo ya halaka wannan kwarto.

Ya dauki sungumi ya yi rijiya. Matarsa kuma na bakin rijiya, ta duba haka sai ta tsinkaye shi da sauri yana sabe da sungumi. Ta gano abin da ya faru. Sai ta rugu da gudu ta tarbo shi tana kiran WAYYO SUN KOMA MAZA. Ya firgita, sai ya soma tambaya. Su Wa? SU WA SUKA KOMA MAZA? Ta ce DUKA MATAN RIJIYA.

Ya yar da sungumi Ya zabura ya ce WALLAHI HAR DA GWAGGO!

Ta sake buga kuwa tana cewa HAR DA ITA?

Ya ce KE BA TA GWAGGO AKE YI BA, INJIN BA KI KOMA NAMIJI BA?

Ta rage kuka ta ce ALLAH YA TSARE INA NAN MACCE TA. Ya ce TO WUCE MU TAFI GIDA.

Idan an kuba, raha kawai mutum zai iya samu a wannan almara. Kuma don haka aka kira ta almarar raha.

Godiya ta musamman ga Jangwarzo.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124