Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 8 | 1M220
==Ma'anar Kwarto==

Ba mu fahintar ma'anar kwarto da kyau sai mun fahinci wani abu tukuna. Wannan abu kuwa shi ne:

1. Karuwa

Idan aka ce karuwa, ana nufin macen da ta bar gidansu ta zauna a wani wuri tana zina da maza suna biyanta.

Kenan kafin mace ta karba sunan karuwa sai ta cika wadannan sharuda:

a. Zama mace

b. Barin gida

c. Karbar kudi don lalata

Idan ba ta cika daya daga wadannan sharuda ba, ba a kiranta karuwa.

A kan wadannan sharuda, kenan babu KARUWI a Hausa, watau ba a ce wa namiji KARUWI, duk kuwa barnar da yake yi, saboda bai cika sharadi na daya ba, watau kasancewa MACE.

2. Danshige

Danshige shi ne namiji mai shiga gidan wani don lalata da wata mace ba tare da amincewar macen ba.

Kafin mutum ya karba sunan danshige, sai ya cika wadannan sharuda:

a. Zama Namiji

b. Shiga gidan wani

c. Tasar wa mace ba da izininta ba

Kenan a bisa wadannan sharuda babu mace 'yarshige.

3. Kwarto

Kwarto na nufin namiji mai hulda da matar wani.

Kafin mutum ya karba sunan kwarto sai ya cika wadannan sharuda:

a. Zama Namiji

b. Hulda da matar wani

Bisa ga wadannan sharuda babu mace kwartanya.

Bambancin Kwarto Da Danshige.

Kwarto da sanin mace yake zuwa, idan ma bai zo ba, ita tana iya zuwa. A takaice kwarto miji ne na karya bayan miji na gaskiya. An lura mace mai miji ita ke kwarto. An lura kuma kwarto babu dole ya je gidan wani, don Macen ma na iya tarar da shi gidansa ko wani wuri. Bahaushe ya ce, "Idan kana rakiyar mace, watarana za ka rake ta gidan kwarto."

Shi kuwa danshige, gidan wani yake shiga. Kuma bai da zabi, yana iya far wa matar wani, ko 'yar wani. A takaice, shige, kokarin fyade ne da ake yi a muhallin wadda aka yi wa. An lura ba a shige sai a cikin gida. Idan mutum ya far wa wata ba a gidansu ba, to ba shige ba ne sai dai fyade.

Wannan bayani fa duka fahinta ce kawai ta MH, babu mamaki akwai gyara a ciki. Amma da yake harshe abu ne na kowa, mutum na iya kara dubawa ya gani, idan akwai wani gyara ko karin bayani sai a yi.

Allah Ya taimaka mana.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124