Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 8 | 1M224
==Yada Billin Takan Yi Billin....==

A wani kacici-kacici ana cewa YADA BILLIN TAKAN YI BILLIN, HAKA BILLIN TAKAN YI BILLIN.

Sai a fassara shi da

YADA KAZA TAKAN YI KWAN NAN, HAKA KWANNAAN YAKAN YI KAZA.

Wasu kuma na fassarawa, kamar sashen su Jangwarzo

YADA KAZA TAKAN YI KOYE, HAKA KOYE YAKAN YI KAZA.

Ina son amfani da wannan kacici-kacici in magana da masu shigowa su ce ba su ga sabon rubutu ba. Sun kasa kila fahintar wannan kacici-kacici, Da sun fahince shi da kyau, da kuwa sun yi rubutu. Idan sun yi rubutu, to rubutunsu zai iya haifuwar wani rubutu. Shikenan sai a yi ta BILLIN BILLIN.

Idan kuma sun ki rubuta kome, kowa ma na iya kin rubutawa. A nan ma sai a yi ta BILLIN BILLIN.

Ka saka a kanka koyaushe ka shigo MH cewa, YADA BILLIN TAKAN YI BILLIN, HAKA BILLIN TAKAN YI BILLIN.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124