Makarantar Hausa
wt 4 | 1M226
==Bankin Mutane==
Idan babu wurin kula da yara a kasarku, to akwai shi a kasar wasu. Haka idan babu wurin kula da tsofi a kasarku to akwai shi a kasar wasu. Abu guda da wata kila ba ka musawa shi ne akwai BANKI a kasarku.
Na sani, ka sani amfanin banki shi ne a adana maka dukiyarka daga kowane hadari, musamman barayi.
To a yanzu mutane sun koma su ne kudi. Su yanzu inda za su boye kansu suke nema. A yanzu mutum na wasa da kansa wani na dauke shi. Don haka a yanzu babban abin boyo ga mutum shi ne kansa, ba wai dukiyarsa ba.
Wannan idan ba Allah Ya gyara ba, wata kila a sami bankin mutane, watau inda za su rika kai kansu don a ajiye masu. Allah Ya tsare. Allah kuma Ya kare.