Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M230
==A Koma Ta Karkashin Kasa==

To, abin dai yanzu kam sai yadda Allah Ya yi. Na fadi haka ne ganin yadda tafiya kasa ta zama wani irin tashin hankali ga mutanen kauye. A da mutum zai iya tafiyar sama da awa uku shi kadai a cikin daji ba tare da wata fargaba ba. A yanzu wannan da kyar ne.

Mutanen birini har ma da na kauye za su iya shiga mota su yi tafiya mai nisa daga wata jaha zawa wata jaha, kuma hankalinsu a kwance, amma a yanzu wannan shi ma ya zama da kyar. Shiga jirgin kasa ya zama wani irin tashin hankali, samun tikitin ma sai mai karfi ko galihu, ko mai tsananin naci. Shi ma kana ciki hankalinka a tashe sai ka ga an sauka.

Masu kudi ba su da wannan damuwa, don jirgin sama kawai za su haye cikin mintuna ko 'yan awoyi sun kai cikin kwanciyar hankali, amma a yanzu kuma babu jirgin. Da kudinka a hannu, amma babu, a yi ma tsada ka ce ka yarda za ka biya amma babu jirgin.

Wani ya ce daga Legas zuwa Gombe sai da ya biya dubu dari biyar aka dauko shi da matarsa da yaransu uku. Kuma da kyar aka sami jirgin.

To ni a ganina dabara guda ita ce mafita, wannan dabar kuwa ita ce a koma bin ta karkashin kasa, amma na san ma ita ma da KYAR!

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124