Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M231
==Ku Sake Shiri==

Har yanzu fa tsugune ba ta kare ba, game da bala'in da muka sha ko kuma muke sha game da Kurona. Ku sake shiri, ko kuma ku kara shi har idan kuna cikinsa. Kun san wahalhalun da muka sha kan wannan cuta, da wadanda har yanzu muke shansu duka kuma dalilinta. Yanzu an ce wani nau'i kuma na Kurona ya bullo, tsoro ya koma kama duniya. Kuma kuna sane da maganin Kurona, watau ko dai a killace ka, ko kuma a rufe ka. Wannan ba karamin bala'i ba ne har idan kana talaka.

Shiri da nake nufi shi ne, ka tanadi dan wani abu ka rika tarawa a gidanka, watau dan abin da za ka ci, ko kuma iyali za su ci, don ba ka san a layin da za ka fada ba. Idan dai an killace ka, dole a ba ka abinci, idan kuwa an kulle ka, babu dole a ba ka kome.

Ku soma shiri kun ji.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124