Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M232
==Allah Daya Gari Bamban==

Na ga wani hoton bidiyo, wanda ke nuna wani mutum a kwance rairan daga shi sai wando. Ga katon turmi an aza a cikinsa, ga mata biyu rike da tabare suna ta daka, kamar dai wanda ake neman a kashe. Ga taron mata ana ta kida suna ta rawa.

Wannan fa al'ada ce ta wannan kabila, idan mutum zai karin mata dole sai an yi masa wannan lugude a kan cikinsa.

Watakila suna yin wannan al'ada ne don su gwada karfin halin namiji, ko kuma don su rage yawan aure-aure, ko kuma don su nuna wa namiji cewa auren mata biyu wani irin tashin hankali ne da ya yi kama da jefa kai a cikin turmi.

Wannan kenan.

Su kuwa Barebari, yadda suke nasu aiki, shi ne, idan mutum zai yi aure ko na fari ko na kari, sukan aza tukunya a kan murhu, a dora abinci, ga ango da amarya a gaban mutane zaune, sai abinci ya dafu, sai a rika debo abincin nan daga cikin tukunyar da ke kan wuta a rika zuba masu a tafukan hannuwa. Duk zafi, babu halin ka yar, haka za ka daure ka saka shi a cikin masayi. Haka za a yi wa kowa har sau uku.

Ana ganin Kanuri na yin wannan ne don su nuna wa ma'aurata su rike aurensu da juriya kamar yadda suka yi juriyar rike wannan abinci mai zafi.

Sam! Ni ba ni ganin haka, Ni ina ganin ana dai yin wannan abin ne don a gwada masu cewa, su bar ganin aure abu mai sanyi, bisa ga hakika abu ne mai zafi sai an daure.

Don sanin al'adun Barebari a kan aure, ana iya duba wannan gudummawa daga BBC HAUSA:

rahotanni-55446444

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124