Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M234
==Allah Ga Wata!==

Mutum bai gane zancena na ALLAH GA WATA, sai ya karanta dan wannan labari na wani mutum:

Wai wani ne ya je hajji, ya sami wani wuri kusa da Dakin Kaba, ya cira hannuwa yana ta rokon Allah babu ji babu gani. Wani mutum da ke kusa da shi, sai ya kura masa ido yana mamakin irin girman matsalarsa. To ko da kuma ya saurara da kyau, sai ya ji mai addu'a na ta cewa "Allah Ka tsare ni daga 'yan sa ido! Allah Ka tsare ni daga 'yan sa ido"!

Da mai saurare ya ji abin da mai addu'a ke cewa sai abin ya kara ba shi mamaki fiye da mamakin da, sai ya dafa kafadarsa ya ce, amma dai kai ba ka san abin da kake yi ba. Yanzu ka kashe zunzurutun kudi ka zo hajji, amma ka rasa abin da za ka roki Allah sai tsari daga 'yan sa ido?

Mai addu'a sai ya kara cira hannaye sama ya kara daga sauti ya ce "Allah ga wani"!

Ma'ana Allah ga wani dan sa ido a nan ma.

To ko gaskiya ne ko kirkira ne wannan labari, ni ban damu ba. abin da ya dame ne shi ne shigowar sabuwar shekara. Na san yadda ta baya muka sha ukuba, muka yi ta addu'a Allah Ya gwada mana ta fita muna da rai. shi ne na ce "Allah ga wata!" Ma'ana ga wata shekara sabuwa, Allah muna rokon Ka yi mana agaji kamar yadda Ka yi mana agaji daga wadda ta fita. Allah Ka sa ma ta fi waccan kyau. Amin.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124