Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M235
==Bikin Shan Rake==

Rake ko arakke wani kare ne mai kauri mai ruwa mai zaki. An ce da shi ake madi da kuma shuga.

A wani wuri, kalmar rake namiji ce, amma a Sakkwato kalmar arakke mace ce.

Ban sani ba ko bikin shan rake sabo ne ko tsoho, amma dai an yi shi a Kano, a wata unguwar da ake kira Unguwar Bello da ke Ɗorayi Ƙarama.

Matasa ne kan yi shi, kuma sun ce wannan shi ne karo na biyu da suka yi irin wannan biki. Nishadi da barkwanci su ne kashin bayan bikin. Sanadinsa, kamar yadda suka ce, murnar sabuwar shekara.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124