Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M237
==Hausa Ce Kawai Hankaka?==

Ana yi wa Hausa kirari da cewa "Hausa hankaka, maida dan wani naki"

A tunanin Bahaushe hankaka kan dauki kwan kaza ko kwan zabo ta je ta kyankyashe ya koma hankaka, wannan tunani ba gaskiya ba ne, to amma ba gaskiyarsa muke son bayani ba. Abin da muke son bayani shi ne wannan kirari na Hausa.

Abin da kirarin ke nufi shi ne, Hausa kan dauki kalmar wani harshe ta jujjuya ta ta koma kamar tata ce ta asali, ta yadda ko masu kalmar da kyar wata rana su iya gane tasu ce. Misali "Aljifu", wannan kalma ce ta Larabci watau "Aljaibu". Da kyar Balarabe ya gane ALJIFU kalmarsa ce aka aro aka yi mata wannan badda kama.

To idan haka ne, ba Hausa ba ce kawai hankaka, harsunan duniya ma gaba daya hankaki ne masu mayar da dan wani nasu. Misali Ingilishi, ya aro kalmomin Larabci na ALIFUN BA'UN TA'UN, gaba-daya ya hade wadannan kalmomi uku ya mayar da su kalma daya ya ce ALPHABET. Idan Balarabe bai karanci Ingilishi ba, da kyar ya gane irin wannan salo na satar kalmomi.

Haka Bahaushe ya aro kalmar MASALLA, daga Larabci mai nufin wurin salla. Ya yi kari ya ce MASALLACI. Shi kuma Bayerabe ya ara daga Hausa, ya jujjuya ya mayar da ita MASOLASHI.

Da dan wannan misali za a gane dai hankaki a duniya yawa ne gare su ba Hausa ba ce kawai hankaka mai mayar da dan wani nata.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124