Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 6 | 1M238
==SARAUTAR HAUSA==

Sarautun gargajiya, ba wai na Hausa kadai ba, ana iya cewa kimarsu na dusashewa saboda zamani. A da, sarki shi ke da wuka da nama game da duk wani abu da ya danganci kasarsa. Yanzu kuwa ba haka abin yake ba, abin yana hannun Gwamnati ne, ko wata sarauta mai kama da Gwamnati.

Hausawa suna da sarautu tun da kamar kowa, kuma duk inda suka sami kansu da kyar su kasa nada SARKI. Ba su cika kiran shugabansu SHUGABA ba, sai dai SARKI. Wannan yana nuna mana irin girman darajar sarauta ga idon Hausa.

Abin da zai ba ka tabbacin wannan magana shi ne, Hausawan da ke kasashen Turai, wadanda ba su kasa dubu talatin, suna da SARKINSU, wanda fadarsa ke FARIS, kuma yana da hakimai a warwatse a wasu manyan kasashen Turai.

Ya wannan sarautar Hausa take a Turai? A duba gudummawar BBC HAUSA:

labarai-55684555

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124