Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 6 | 1M240
==Ido Wa Ka Raina?==

Bahaushe ya ce an tambayi ido da cewa WA YA RAINA? Ya bayar da amsa da cewa WANDA NAKE GANI KULLUM.

Wannan karin magana na bayyana mana daliln da ke kawo raini, watau sabawa da ganin abu.

Duk abin da kake gani, kimarsa da tsoronsa da duk wani abu nasa za su iya raguwa ko fita ma daga kwakwalwarka. Amma idan ba ka cika ganinsa ba, ko ma ba ka taba ganinsa ba, za ka ga girmansa, ko tsaron ko mamakinsa ko wani abu da yake da shi.

Misali, a ce maka akwai wani abu wanda bai da wani wurin zama, amma wasu abubuwa na iya haduwa kawai sai a gan shi ya fito a tsakaninsu dan tsirit. Kana kallonsa yana kara girma a hankali a hankali, idan ba gusa ba, sai ya dauke ka ya cinye. Bayan ya cinye ka, idan ba a yi hankali ba, sai ya cinye dakinka, da gidanka da garinku, da kasarku, idan ya ga babu wani abu da zai ci sai ya cinye kansa ya koma babu!

Mutum zai yi mamakin irin wannan abu, amma da ya ji an ce WUTA, zai tuna ya san tana iya haka, amma sai ya bar mamaki don ya yi ta ganinta da irin ayukanta.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124