Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 6 | 1M241
==A Sa Allo, Ko A Kara Gidajen Yari==

Idan na ce ALLO, ina nufin allon da ake kafawa a tituna, don tallata abu, ko don wayar da kai a kan wani abu.

Wannan rubutu yana magana ne kan wata doka da aka kafa mai nuni da cewa saba ka'idar Kurona zai sa a garkame mutum a gidan yari har na tsawon wata shida.

Ban sani ba, dokar ta soma aiki ko ba ta soma ba. Idan ba ta soma ba, to ya kamata a kakkafa alluna masu yin gargadi. Misali "RASHIN TAKUNKUMI, ZAMAN GIDAN YARI WATA SHIDA"

Yin haka wata kila ya sa mutane su ankara da wani bala'i da ke gabansu bayan bala'in da suke ciki na Kurona ita kanta.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124