Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 6 | 1M244
==Gadon Mata==

Idan aka ce gado, ana nufin abin mamaci kan bari.

Akwai takaddama wajen rabon gado a cikin al'umma da dama a yanzu. Ina nufin tsakanin mata da maza.

Ba a je nesa ba, a cikin Hausawa na da, babban da shi ke rike gida, ba a cika rabawa ba, sai a yi ta tafiya da gidan da dukiyar mahaifi a karkashin kulawar babban da. Sauran 'ya'ya kuma za su samu kulawa daga yayansu, kamar yadda suke samu daga mahafinsu.

Mata su ne suka fi rashin samun kome na gado, sai dai za su samu kulawa irin ta mahaifinsu.

A yanzu da Bahaushe ya kama Musulunci sosai ana rabawa a bai wa kowa nasa kaso, sai dai ana iya hadewa kuma a saka a karkashin babban da. Amma wannan ya fi aukuwa a birane ko a mayan kauyuka. Amma a kananan kauyuka har yanzu akwai abin da ba a rabawa da mata, kamar gida da gona. To amma fa dole mata su sami cikakkiyar kulawa daga mazan da suka mamaye kome.

To amma abin, watakila ba haka yake a kabilar Igbo ba, inda maza aka ce suna mamaye gado ba tare da bada cikakkiyar kulawa ga mata ba. A duba wannan gudummaea ta BBC HAUSA, don a ga yadda gado yake a kabilar Igbo.

rahotanni-55901138

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124