Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 6 | 1M245
==An Ce Dujjal Ya Bayyana?==

Ba ka rabuwa da jin labarai iri-iri. Da na gaskiya da wadanda sai dai ka ji kawai ka yi shuru.

A dazu ne da safe wata ke tambayata da cewa, WAI DUJJAL YA BAYYANA? NA ce Wallahi ban sani ba! Sai ta ce to in yi sauri in saurari radiyo! Ni dai abin sai mamaki yake ba ni. Ta kara da cewa HAU INTANET KA GANI! Da na rasa ta cewa sai na ce, bayyanar Dujjal ta fi karfin a ji ta a radiyo ko a gan ta ga intanet.

Amma fa ban sani ba kai mai karatu ko kana da wannan labari. Ni dai Wallahi ban da shi! Amma fa a kula, ba bayyanar Dujjal nake musu ba, a'a, ni dai kawai ban da labarin ya bayyana ne a yau Talata.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124