Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 5 | 1M247
==Gudummawar Turawa==

Wannan amsa ce ga tambaya mai lamba

1141M1 wadda take tambaya ga alama a kan ayukan Nahawun Hausa da suka gabaci shahararren aikin F.W Parsons a kan aikatau na Hausa.

To Malam Abubakar, wannan tambaya babba ce, don tana nufin komawa baya zuwa ga karni na sha takwas zuwa na ashirin. Wannan Bataure an yi shi ne a karni na ashirin, nazarin Hausa kuwa an fara shi ne tun a karni na sha takwas.

Makarantar Hausa na da salon karba tambaya guda biyu. Na farko ta karba tambaya kai-tsaye idan tambayar mai sauki ce. Na biyu ta aza mai tambaya bisa ga hanyar da take zaton zai samo amsa da kansa. Wannan amsa taka tana bisa wannan salo.

Akwai ayuka guda uku da za ka nema ka duba,

1. Hausa A Rubuce...

Wannan littafi ne Na Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, daga cikin abin da ya kawo, akwai ayukan Turawa tun a karni na sha tawkas, a ciki sai ka zabi ayukan da suka riga na Parsons ka duba masu alaka da Nahawun Hausa.

2. Baje Kolin Rubutun Hausa

Wannan wata makala ce da Farfesa Dahiru Muhammad Argungu ya rubuta. Ta kunshi sunayen ayuka masu yawa game da Hausa, watau kamar kari ne game da abin da aiki na Yahaya ya tattara. Ka duba wannan takarda babu mamaki ka sami ayukan Nahawun Hausa da suka gabaci na Parsons.

3. Gudummawar Turawa...

Wannan takarda ce da Farfesa Amfani ya gabatar, tana dauke da ayukan da Turawa suka yi a kan Harshen Hausa, a ciki za ka iya samun wadanda suka gabaci na shi Parsons din.

Allah Ya taimaka mana gaba-daya


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124