Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M3
Ku yi wa masu waka albishir da cewa nan da sati daya za su samu wata garabasa da Makarantar Hausa ta tanada don biyan bukatarsu kawai.

An sani babban abin da ke bai wa marubucin wakoki masu kafiya shi ne kafiyar da za ta dace da 'yan'uwanta. Da yawa mawaki kan soma baiti, amma kafiya ta tsaya ta ki tafowa. To daga sati mai zuwa wannan wahala an daina yinta. An daina jiran kafiya har ta tafo. Shigowa kawai za ka yi Makarantar Hausa ka sa GABAR SAUTIN da kake bukatar kafiya da shi. a ba ka shi duk inda yake, ko a mafi yawan inda yake a kalmomin Hausa.

A jira sati mai zuwa a ga abin mamaki.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124