Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M5
A jiya aka ba ni labarin cewa wani gidan radiyo a Sakkwato ya yi mahawara a kan ma'anar karin magana din nan mai cewa DUNIYA ZAMAN 'YAN MARIMA.

Ma'anar wannan karin magana yana iya yin wuya ga yaran zamani wadanda ba su san yadda ake yin sana'ar rini ba a da.

Sana'ar rini sana'a ce da ake yi don canja wa tufa launi. Mai sana'ar ana ce masa MARINI. Idan suna da yawa a ce MARINA. Wurin da ake sana'ar a ce masa MARINA.

To a lokacin da wadannan masu sana'ar ke aikinsu, kowa yana kallon jihar da ya ga dama ne, ba sahu suke yi ba su kalli jiha daya. Watau kowa da inda yake kallo ko yake huskanta.

To Bahaushe yana son ya nuna harkar duniya haka take. Kowane mutum da harkar da ya sa gaba, ta wani ba irin ta wani ba ce, kowa da tasa harka. Kowa da tasa manufa.

Wannan shi ne ma'anar wannan karin magana.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124