Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M50
==Sabuwar Al'ada==

Tabbas saura kiris a sami wata sabuwar Al'ada a cikin Hausawa. Wannan sabuwar Al'ada kuwa da ke shirin bulla, ita ce canjin suna.

A al'adance zana suna ana yinsa sau daya ne a rayuwa. Duk da yake idan an sami sabani tsakanin dangin yaro ana iya samun wannan canji. Na taba jin wannan sau daya. To amma abin da ban taba ji ba shi ne haka kawai mahaifi ya bushi iska, ya tara mutane ya yanka dabba ya canja wa dansa suna. An ce kuma an sami wannan abu sau biyu a cikin sati daya! An yi haka a Kano, kuma an yi haka a Katsina.

To idan wannan al'ada ta sami karbuwa, Nan da wasu shekaru kadan dattijo ma zai sauya wa kansa suna. Tunda a tunanin masu yin haka, suna ganin tara mutane da yanka rago shi ne samun suna. Idan haka ya faru, mutum daya zai iya samun suna ashirin shi daya matsawar yana da kudin raguna. Wata kila, za ka iya sanin mutum sunansa Usman a shekarar 2019, amma a shekarar 2029, Idan kuka hadu ka ce "Usman ne", sai ya ce "Amma a da", amma a yanzu "Isma'il" ne.

Duba wannan abu a BBC Hausa

labarai-50806553

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124