Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M54
==Me Ya Yi Zafi?==

Wani mamba ya yi korafi cewa ya zabi wani mamba, amma kuma ya koma ganinsa a MAMBOBI MASU JIRAN ZABE.

Bayan nazari mai tsawo MH ta gano ba shafinta ke da matsala ba. Wannan mamba ya bude akawun ne sau biyu:

Na daya yana da lamba

1009

Na biyu yana da lamba 1020

Ko kadan haka bai dace ba. Idan mutum ya riga ya yi rijista a farko, to idan zai koma shiga yakan shiga ne a TSOHON MAMBA. Idan kuma ya manta fasiwot dinsa sai ya neme ta a NA MANTA FASIWOT. Wadannan abubuwa duka suna nan a farkon shafin MH. Idan duka abin ya ci tura, ana iya tuntubar MH ta wayarta.

Buda akawun biyu, kamar mutum yana son raba hankalin mazabansa ne, sannan kuma zai rikitar da masu neman rubutunsa. Misali idan ka shiga @1009 za ka sami rubutu mai yawa amma idan ka shiga @1020 babu kome a ciki a lokacin wannan rubutu.

Shawara:

Mai akawun biyu yana da dama ya rike abinsa, kuma yana da damar neman MH ta rafe daya.

Idan mutum na son rufe akawun dinsa, zai rubuto ne a Magama cewa yana son a rufe, amma da sharadin cewa duk wani rubutu mai amfani da ke cikinsa ya zama na MH. Sannan idan yana da kudi a asusu kowane iri, da katinsa da ya kirkira idan ya kirkira, duka ya yi hasararsu.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124